3 Yuli 2014 - 11:34
Iraki: An Hallaka Wani Babban Kwamandan 'Yan Ta'adda Na ISIL A Fallujah

Majiyoyin tsaro a kasar Iraki sun tabbatar da kashe Abul-ala Al-shami, mutumin da ke harhada nakiyoyin da 'yan kunar bakin wake ke kai hare-hare da su a sassa daban-daban na kasar.

Majiyoyin suka ce an kashe Abul-ala ne a jiya a garin Falluja tare da wasu mutane 4 da suke tare da shi da suke shirin kai wasu hare-haren kunar bakin wake, kafin wannan lokacin dai Abul-ala wanda dan kasar Syria ne ya kasance babban kwamandan kungiyar 'yan ta'adda ta ISIS a garin Dar'a, daga bisani kuma ya daw cikin kasar Iraki domin shirya hare-haren kunar bakin wake da ake kaiwa a kan jami'an tsaro da kuma fararen hula a kasar.

A bangare guda kuma gwamnatin Iraki ta sha alwashin gurfanar da  gwamnatocin da ke da hannu wajen daukar nauyin tura 'yan ta'adda a cikin kasar a gaban kotun manyan manyan lafuka ta duniya, inda majiyoyin gwamnatin Iraki suka ce yanzu haka ana harhada tabbatattun hujjoji kan rawar da wasu kasashen larabawa suke takawa wajen daukar nauyin ayyukan ta'addanci a cikin kasar Iraki, wadanda za a gabatarwa majalsar dnin duniya da kuma kotun manyan laifuka ta kasa da kasa.ABNA